fidelitybank

Yadda aka yi jana’izar mutane 15 da Lakurawa su ka kashe a Kebbi

Date:

An gudanar da jana’izar mutanen da Lakurawa suka kashe a garin Mera na jihar Kebbi.

A ranar Juma’a da rana ne dai aka samu arangama tsakanin mutanen gari da Lakuwaran a wajen garin Mera na jihar Kebbi.

An samu arangamar ne dai bayan da aka zargi Lakuwaran da ƙwace wa wani mutumin gari Mera dabbobin da ke yake kiwo a wajen garin, lamarin da ya sa ‘yan garin suka fusata, suka kuma fita bayan gari da nufin yin arangama da Lakuwaran domin ƙwato dabbobin.

Arangamar ta haifar da asarar rayuka da jikkata daga mutanen garin da kuma ɓangaren Lakuwaran, kamar yadda wani ɗan jarida ya tabbatar wa BBC.

Cikin waɗanda suka halarci jana’izar har da mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida tare da Maimartaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera.

A cikin makon nan ne dai hadikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da ɓullar ƙungiyar Lakurawan, bayan da mazauna yankin suka koka game da ayyukan ‘yan ƙungiyar, waɗanda ke ƙwace wa mutane dabbobi da nufin samun ”ganima” ko fitar da ”zakka”.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp