An ci gaba da zaman sauraron karafin da jam’iyyun adawa suka shigar gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe domin ƙalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
Wakilin BBC da ke harabar kotun ya ce, an jibge jami’an tsaro na ‘yan sanda a mahaɗar hanyar da za ta sada ka da babbar kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja inda ake zaman sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar.
An kuma rufe hanyar da ta bi ta gaban kotun, sannan an hana mutane wucewa sai waɗanda ke aiki a cikin kotun.
Sannan ba a barin kowa ya shiga cikin kotun harda ‘yan jarida, sai dai waɗanda kawai aka tantance.
Haka kuma akwai tarin ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya na DSS da ke ciki da wajen harabar kotun, domin tabbatar da tsaro a yayin sauraron ƙarar.