Ƙasashe da dama a nahiyar Turai da Afirka sun gudanar da bikin tarbar sabuwar shekara ta 2023.
Mutane dai sun mamaye titunan manyan birane daga Warsaw da Stockholm a gabashi, zuwa Brussels da Paris da Madrid da birnin London.
An taƙaita bukukuwan zuwan sabuwar shekara shekaru biyu da suka gabata saboda annobar korona.
An dai gudanar da bukukuwan murna a kasashen Gabas ta Tsakiya da Asiya.
An kuma fara gudanar da shagulgulan sabuwar shekarar a ƙasashen nahiyar Amurka.