A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu’o’i ga marigayi shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a taron majalisar zartaswa da ake gudanarwa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Manyan jami’an gwamnati da dama ne suka halarci taron addu’o’in, ciki har da wasu daga cikin ƴaƴan marigayin.
Yusuf Buhari, wanda shi kaɗai ne ɗa namiji a wajen marigayin.
Ƴaƴan marigayin da suka halarci taron sun haɗa da Yusuf Buhari da Fatima Buhari da Hadiza Buhari da kuma Halima Buhari.
Yusuf Buhari ya ce sun ji daɗin jana’iza ta girmamawa da aka yi wa mahaifin nasu kuma “hakan ya nuna cewa ba ɗan siyasa kawai aka ɗauki mahaifin namu ba, an ɗauke shi matsayin aboki kuma uba.
An yi zaman hadin gwiwa ne tsakanin ɓangarorin gwamnati uku, ɓangaren zartarwa da majalisa da kuma fannin shari’a.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya jagoranci iyalan Buhari zuwa fadar shugaban ƙasar.