A wurare da dama a Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya, an baza jami’an tsaro domin jiran kota-kwana.
Matasa dai sun kira a gudanar da zanga-zangar lumana a yau domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma abin da suka ce rashin iya gudanar da tattalin arziki karkashin gwamnatin Tinubu.
Sai dai tabanin yadda suka yi ta yekuwa a shafukan sada zumunta, zanga-zangar ta yau ba ta yi armashi ba.


