Ministar al’adu ta Najeriya, Hannatu Musawa ta ce ya kamata shugabancin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ƴan kudancin Najeriya a wa’adin mulki mai zuwa domin tabbatar da daidaito da adalci.
Kodayake kundin tsarin mulkin Najeriya, bai yi tanadinsa ba, manyan jam’iyyun ƙasar na bin tsarin karɓa-karɓa tsakani kudanci da arewacin ƙasar.
Cikin wata hira da gidan talbijin na Channels ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce ya kamata mulki ya ci gaba da zama a hannun ƴan kudancin ƙasar indai adalci ake son yi.
A shekarar 2023 ne Shugaba Tinubu – wanda ɗan kudancin ƙasar ne – ya karɓi mulki daga Muhamamdu Buhari ɗan arewaci – da ya shafe shekara takwas a kan karagar mulki.
“Abu ne na fahimta, bayan shekara takwas na Buhari daga arewa ya kamata su ma ƴan kudu su yi shekara takwas, domin samar da adalci”, in ji ministar
A baya-bayan nan ma an ambato tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom na cewa ba zai goyi bayan ɗan takara daga arewacin ƙasar ba.
Batun karɓa-karɓa tsakanin arewaci da kudancin Najeriya, wani al’amari da aka jima ana muhawara kansa a fagen siyasar Najeriya.
Wani abu da masana ke cewa yana mayar da tsarin dimokraɗiyyar ƙasar baya.