fidelitybank

Ya kamata Buhari ya ɗaure ni da sauran ƴan siyasa — Tsohon Minista

Date:

 

 

 

 

Tsohon Ministan Aiyuka, Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya sanya kansa a cikin ƴan siyasar da ya kamata a hukunta su sakamakon zagon-ƙasa da su ka yi wa Nijeriya ta hanyar sace kuɗaɗen gwamnati.

Da a ke zanta wa da shi a wani shiri a tashar rediyo ta Radio France International, Kazaure ya ce duk ƴan siyasar Nijeriya ɗaya su ke, inda ya ce babu wani wanda ya ke yi don talakawa.

A cewar sa, ya faɗa wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya kame duk ƴan siyasar da su ka wawashe kuɗaɗen gwamnati har da shi.

Tsohon Ministan ya ce duk ƴan siyasan da su ka rike madafun iko tun daga 1999 ba su yi wa ƙasar komai ba.

“Har ni da na ke wannan maganar, ya kamata a ɗaure mu sabo da ba mu yi wa ƙasar nan komai ba

“Na sha faɗin cewa ni Ibrahim Musa Kazaure, mun zalunci Nijeriya da talakawan ta.

“Magana ta gaskiya ita ce, dukkan mu kanwar ja ce. Abin da mu ka yi wa Nijeriya ba haka ya dace mu yi mata ba sabo da wasu daga cikin mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba.

“Ni dai gaskiya na faɗa. Dukkkan mu da mu ka yi sata, a matse mu mu dawo da kuɗaɗen da mu ka sata. Na faɗa wa Buhari, a kame mu a ɗaure mu har sai mun dawo da kuɗaɗen da mu ka sata.

“Ni ba zan sake karɓar wani muƙami a kasar nan ba, ko da kyauta ne,” in ji Kazaure.

 

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp