Gwamnatin Birtaniya ta dauki matakin ladabtarwa kan mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich a karkashin martaninta kan mamayar da Rasha ke yi wa kasar Ukraine.
Yana cikin manyan attajirai bakwai da Birtaniyar za ta kakaba wa sabbin matakan ladabtarwa, ciki har da kwace kadarorinsa da hana shi tafiye-tafiye.
Cikin attajiran da wannan matakin zai shafa akwai Igor Sechin da Oleg Deripaska, wadanda ake kallo a matsayin makusantan Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce “babu maboya” ga wadanda ke ba wannan mamayar goyon baya.
Gwamnatinsa ta sha matsin lamba domi ta dauki mataki kan Mista Abramovich, wanda ya ce ya yanke shawarar sayar da kungiyarsa ta Chelsea a farkon wannan watan.
BBC ta rawaito cewa, a na hasashen Abramovich mai shekara 55 na hannun daman Vladimir Putin ne, hasashen da ya musanta, inda ake kuma ganin Abramovich na da arzikin da