Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa, yakin da ake yi a Ukraine yana kara jefa duniya cikin hadarin karancin abinci da kuma yunwa a watannin da ke tafe.
Da yake magana a taron kolin Majalisar a New York, Antonio Guterres ya ce kutsen na Rasha, ya sake ta’azzara matsalar karancin abinci, wadda daman tuni matsalar karuwar yanayin zafi a duniya da kuma annobar korona suka shafa.
Majalisar ta ce a cikin shekara biyu kadai yawan mutanen da ke fama da karancin abincin ya ninka biyu daga miliyan 135 zuwa miliyan 276, a yau.
Cibiyoyin kudi na duniya, da suka hada da Bankin Duniya sun sanar da bayar da tallafin biliyoyin dala domin sassauta lamarin.