Bayer Leverkusen ta nada Xabi Alonso a matsayin sabon kocinta bayan ta kori Gerardo Seoane.
Kulob din Bundesliga ya sanar a ranar Laraba cewa sun “rabu” da Seaone.
An maye gurbinsa da Alonso, mai shekaru 40, wanda zai rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa watan Yunin 2024.
Wasan karshe da Seoane ya jagoranta shi ne rashin nasara da ci 2-0 a Porto a gasar zakarun Turai ranar Talata, kwanaki bayan da aka doke su da ci 4-0 a Bayern Munich a gasar.
Alonso dai bai da aiki tun bayan barinsa Real Sociedad B a watan Mayu bayan ya shafe shekaru uku yana horarwa.
Leverkusen ita ce ta biyu daga kasan teburin gasar ta Jamus da maki biyar kacal daga wasannin takwas na farko.