Wani matashi wanda har yanzu ba a tantance ko wanene ba, ya mutu a lokacin da yake kokarin dauke wasu igiyoyin wuta daga na’urar taransfoma a yankin Okija da ke jihar Anambra.
Naija News ta rawaito cewa, wutar lantarki ne ya kashe shi a lokacin da yake kokarin sace kayan Rarraba mai karfin 500KVA a kauyen Umuatuegwu yayin da abokansa suka tsere daga wurin.
Sanarwar da Shugaban Kamfanin Sadarwa na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Enugu (EEDC), Emeka Ezeh ya fitar, ya tabbatar da cewa, barayin sun kutsa cikin kadarorin kamfanin da misalin karfe 6:00 na safiyar Lahadi.
Ezeh ya kuma ce, sauran ‘yan kungiyar sun tsere daga inda lamarin ya faru, bayan da suka ga wutar lantarki ta kama abokin aikinsu, inda suka bar gawarsa da kayan aikinsu.
Ya ƙara da cewar, an kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda na Okija, domin yin cikakken bincike.