An dawo da hasken wutar lantaki a akasarin biranen Najeriya da suka fada cikin duhu sakamakon lalacewar babban layin samar da wuta na kasa a ranar Lahadi.
Lalacewar babban layin ya haifar da rashin hasken wutar lantarki a manyan biranen kasar har da Abuja, babban birnin Najeriya.
Kamfanonin samar da wutar lantarki a sassan kasar sun aika sakon bai wa abokanan huldarsu hakuri game da rashin wutar.
Cikin wata sanarwa, kamfanin rarraba lantarki na Najeriya ya sanar da gyaran babban layin wutar lantarkin bayan aikin da aka yi a kai.
Wannan ne karon farko da babban layin lantarkin ya samu matsala a wannan shekarar. A bara, ya sha fuskantar matsaloli lokuta da dama.
Najeriya da ke da yawan al’umma na fiye da mutum miliyan 200, har yanzu tana iya samar da wutar lantarki tsakanin megawatts 3500 da 4500.
Duk da kasancewar ta kasa mai arzikin mai da iskar gas, har yanzu ba a samar da tsayayyiyar wutar lantarki.