fidelitybank

Wolves ta nada Garry O’Neil a matsayin mai horas da ita

Date:

Wolverhampton ta sanar da nada tsohon kociyan Bournemouth, Garry O’Neil, a matsayin wanda zai horar da ita.

Tuni ya amince da kwantiragin kaka uku, ya kuma maye gurbin Julen Lopetegui.

An sanar da raba gari tsakanin kungiyar da Lopetegi a Molineu ranar Talata, kwana uku kafin fara kakar Premier League ta 2023/24.

O’Neil ya ja ragamar Bournemouth zuwa mataki na 15 a teburin Premier League a bara, daga baya ta kore shi ranar 19 ga watan Yuni.

Mai shekara 40, shi ne kociyan Wolves na hudu cikin shekara biyu.

Zai fara aiki ranar Litinin, lokacin da Wolves za ta ziyarci Old Trafford domin karawa da Manchester United a wasan farko na Premier League.

Kociyoyi da dama sun nemi aikin horar da Wolves domin maye gurbin Lopetegui, amma O’Neil aka zaba.

Za a fara wasan farko a kakar Premier League ta bana da wasan Burnley, wadda za ta karbi bakuncin Manchester City.

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp