Kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton Wanderers ta amince ta biya yuro miiyan 4.4 domin ɗauko ɗan wasan Paris St-Germain, Pablo Sarabia.
Ɗan wasan mai shekara 30 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da rabi, inda za a gwada lafiyarsa a ranar Talata. Shi ne ɗan wasa na uku da kungiyar ta ɗauka a bana.
Ya koma PSG ne daga Sevilla a 2019 inda ya zura kwallo 11 a wasa 35 da ya buga a gasar Ligue 1.
Sarabia ya shafe kakar 2021-22 a matsayin ɗan aro a Sporting Lisbon, inda ya buga wa Spain wasa ɗaya a gasar cin kofin duniya da aka kammala.
Tun lokacin da ya fara buga wa Sifaniya wasanni a shekarar 2019 ,ya samu nasara a wasa 26, inda ya zura kwallaye tara.
Ɗan wasan sananne ne a wajen kocin Wolves Julen Lopetegui saboda ya horar da shi lokacin da yake kocin Sevilla.
Sai dai Sarabia bai taba buga wasa ba a karkashin Lopetegui lokacin da yake kocin Sevilla kafin ya koma PSG.