Babban jarumain fina-finan Amurka Will Smith ya kira matashin nan dan kasar Guinea da ya je jami’ar Al-azar bayan ratsa kashen Afirka a kan keke.
A shekarar da ta gabata ne Mamadou Safayou Barry ya shiga kanun labarai bayan shafe kilomita kimanin 4,000 a kan keke.
Cikin kiran bidiyon da Smith ya yi wa matashin a birnin Alqahira, inda yake karatu, Smith ya fada masa cewa ya yaba da kokarin da ya yi sannan ya ba shi kyautar sabon keke da laptop.
“Ina son duniya ta ji labarinka,” in ji jarumin.
Cikin wani takaitaccen bidiyo da aka dora a shafin YouTube na Smith, an nuna yadda dalibin yake magana da mutanen da ke zagaye da shi cikin zakuwa yana cewa ”Wannan shi ne Will Smith” in ji Barry, ‘Ina son fina-finanka.
“Ban san yadda zan gode maka ba wallahi ,” in ji matashin bayan da ya ji kyautar.
A watan satumba ne tawagar yaran jarumin ta tuntubi BBC bayan wallafa labarin tafiyar matashin suna masu cewa labarin ya sosa zuciyar jarumin, don haka suna son yin magana da shi.
A watan Mayun shekarar da ta gabata ne Mamadou Safayou Barry mai shekara 25 ya fara tafiyar daga asar Guinea da ke Yammacin Afirka zuwa fitacciyar jami’ar Al-Azhar tare da fatan cewa jami’ar za ta yi maraba da shi.
Mista Barry wanda ke da aure da daya ba zai iya biyan kudin jirgi ba, don haka ne ya dauki kekensa inda ya yi tafiyar wata hudu inda ya ratsa kasashen Maliu da Burkina Faso ta Togo da Benin da Nijar da kuma Chadi.
Ya yi doguwar tafiyar ne ta hanyar ratsa yankunan da ke fama da yake-yaken masu ikirarin jihadi, da kasashen da suka fusknacoi juyin mulkin soji.
Ya sha kamu tare da tsarewa har sau uku ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, sau biyu a Burkina Faso da kuma sau daya a Togo.

Tafiyar Mista Barry ta samu armashi ne a lokacin da ya isa Chadi, inda wani dan jarida ya yi hira da shi sannan ya dora labarinsa a intanet, lamrin da ya sa wata kungiya ta biya masa kudin jirgi domin isa Masar.
Bayan isarsa ne kuma jami’ar Al-Azhar ta ba shi gurbin karatu, da fari a fannin ilimin addinin musulunci, sannan daga baya aka ba shi gurbi a fannin fasaha a kyauta.


