Jam’iyyar PDP a jihar Ribas, ta yi watsi da ikirarin da gwamnan jihar, Nyesom Wike ya yi na cewa ya haramtawa mambobinta yin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar a jihar.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar, Tambari Gbara, ya jaddada cewa, Wike bai taba haramtawa jiga-jigan jam’iyyar yakin neman zaben Wike a jihar Ribas ba.
Gbara yana maida martani ne kan ikirarin da wani tsohon Sanata mai wakiltar Ribas ta Kudu maso Gabas, Ledogo Maeba ya yi na cewa Wike ya gargadi wasu jiga-jigan jam’iyyar kan yi wa Atiku kamfen a jihar.
Maeba ya ce, Wike ya yi wannan gargadin ne bayan da shi da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka ziyarci Atiku inda suka nemi gafara a madadin gwamnan.
Tsohon dan majalisar ya ce, gwamnan ya tsawatar da su kan ziyarar Atiku ba tare da amincewar sa ba.
Maeba ya ce, Wike ya kuma yi barazanar cewa, duk wanda ya yi wa Atiku yakin neman zabe a jihar Ribas ba tare da izininsa ba za a hukunta shi.
Sai dai Gbara ya kalubalanci Maeba da ya tabbatar da zarginsa da cewa Wike ya bayar da barazana ga duk wanda ke yiwa Atiku yakin neman zabe a jihar.
A cikin wata sanarwa, Gbara ya ce: “Idan har gwamnan yana son yin wannan magana, zai bayyana a hukumance, cewa, a jihar, kada wani ya yi wa Atiku Abubakar yakin neman zabe.