fidelitybank

Wike ya zama karfen kafa a wajen gwamnonin PDP bayan jagorancin jam’iyyar a Rivers da ya samu

Date:

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya samu nasarar tabbatar da matsayinsa na madugun PDP na Rivers bayan da kwamitin zantarwa NWC ta amince da tsagen shi na zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyyar PDP na jihar, wanda hakan ya nuna cewa wato Wike ya samu nasara kan gwamnonin PDP.

An yanke wannan shawarar ne a yayin wani taro a hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa da ke Wadata Plaza, Abuja, a ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugaban jam’iyyar, Umar Damagum.

Kwamitin NWC dai ba ta yi taro na tsawon mako uku ba saboda tashe-tashen hankula da ake fama da su musamman tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas Wike da Ƙungiyar Gwamnonin PDP dangane da zaɓen shugabannin PDP na jihar Ribas.

Rikicin ya ɓarke ne a ranar 24 ga watan Agusta inda gwamnonin PDP suka fito ƙarara suka goyi bayan gwamnan jihar Ribas mai ci, Siminalayi Fubara, inda suka yi kira da a sake duba zaɓen shugabannin jihar tare da tabbatar da shugabancin Fubara a jihar.

Wannan goyan bayan ya fusata Wike, wanda a ranar 31 ga watan Agusta ya yi barazanar tayar da tarzoma a jihohin gwamnonin idan suka ci gaba da tsoma baki a harkokin jihar Ribas.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp