Jami’an hukumar babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata, sun ruguza wata haramtacciyar kasuwa mai suna “Kasuwan Dare,” wadanda ake zargi da kasancewa maboyar bata gari da masu sayar da muggan kwayoyi a Asokoro, Abuja.
Kasuwar ta kasance a titin Hassan Musa Katsina, kusa da Kpaduma II a Extension Asokoro, Abuja.
Da yake jawabi bayan rugujewar, Daraktan Sashen Kula da Cigaban Kasa, Mista Mukhtar Galadima, ya ce haramtacciyar kasuwar tana zama barazana ga mazauna yankin da masu wucewa.
Galadima ya kara da cewa an mayar da yankin mafakar aikata miyagun laifuka duk da kokarin da hukumar babban birnin tarayya ta yi na tsaftace yankin.
Ya kara da cewa ’yan bata-gari da ke gudanar da ayyukansu a yankin na yin illa ga kyawon muhallin baki daya, inda ya ce FCTA ba za ta bari ta ci gaba ba.
“Aikin zai taimaka mana wajen kawar da ‘yan iska da masu safarar miyagun kwayoyi da suka mamaye wurin. Mun rusa wurin kusan sau uku, amma sun sake yin gini, suka ci gaba da ayyukansu.
“A wannan karon, kasuwar da aka ruguje za ta ci gaba da rushewa. Muna buƙatar tsaftace wurin kuma mu haɓaka kyawun yanayin muhalli.
“Haka kuma yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tsaftar gari, kuma wannan yana daya daga cikin wuraren da muka fara atisayen,” in ji shi.
Sakataren hukumar ta FCTA, Mista Peter Olumuji, ya ce za a yi kokarin tabbatar da tsaron lafiyar mazauna yankin.
Hakimin kauyen Kpaduma, Mista Bitrus Yakubu, ya yabawa hukumar babban birnin tarayya Abuja bisa kawo musu dauki da kuma kawar da barayin.
“Wurin ya shafe sama da shekaru 20 a nan, amma yau ya gangaro don amfanin kanmu. Mun yi matukar farin ciki a matsayinmu na al’umma cewa an share yankin da kyau,” in ji Yakubu.


