Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi watsi da ikirarin cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na shirin ficewa daga jam’iyyar.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce Wike muhimmin dan jam’iyyar ne kuma mai aminci.
Ologunagba ya ce gwamnan ya zuba jari sosai a PDP don tunanin ficewa daga jam’iyyar.
Wike dai ya fusata ne tun bayan zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin dan takararta.
Ana kyautata zaton gwamnan ya ji takaicin yadda Atiku ya yi biris da shi ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa.
Ya kasance yana tare da jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Wannan ya haifar da yakinin cewa Wike na iya ficewa daga PDP ko kuma ya yi wa jam’iyyar adawa a 2023.
Sai dai, Ologunagba, a cikin wata sanarwa ya ce: “Gwamna Wike muhimmin dan jam’iyyar ne. Mutum ne da ya zuba jari mai yawa a wannan jam’iyya. Ya kuma girbe da yawa daga jam’iyyar; jam’iyyar kuma ta kara masa girma.


