Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Alhamis ya yi kiran taron gaggawa na masu ruwa da tsaki na jamâiyyar PDP reshen jihar.
Wannan dai shi ne irinsa na farko tun bayan dambarwar neman shugabancinsa da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar a fadin kasar.
Duk da cewa ba a bayyana ajandar taron ba, amma hakan ba zai rasa nasaba da umarnin jihar kan mataki na gaba ba, bayan da Wike da tawagarsa suka fice daga majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. .
Wadanda aka gayyata zuwa taron dai sun hada da shugabannin jamâiyyar, âyan majalisar zartarwa na jiha, shugabannin kananan hukumomin jamâiyyar da wasu âyan jiga-jigan jamâiyyar.
Ku tuna cewa gwamnan da ya yi imanin cewa an ci amanar sa ne biyo bayan sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa da kuma na Atiku a yayin da ya ke zabar mataimakinsa a zaben shugaban kasa ya sha alwashin yin magana kan wasu batutuwan da suka haddasa rikicin.
Har ila yau, an ambato Wike yana cewa, “Babu wani abu da ya faru tukuna, amma wani abu zai faru nan ba da jimawa ba.”
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, wadanda aka gayyata na ci gaba da isa gidan gwamnatin jihar Ribas.