Gwamnan River Nyesom Wike ya jaddada goyon bayansa ga Alhaji Atiku Abubakar wanda PDP ta tsayar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Tun a wajen taron PDP Gwamna Wike a cikin jawabinsa ya bayyana cewa zai goyi bayan duk wanda ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani.
“Ba za mu yi watsi da PDP ba, za mu bayar da cikakken goyon baya ga Atiku Abubakar,” kamar yadda Wike ya bayyana a shafinsa na Facebook.