Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi kira ga gwamna Siminalayi Fubara da ya yi biyayya ga hukuncin kotu idan yana son zaman lafiya a jihar.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata a tashar talabijin ta Channels, inda ya ce, “zaman lafiya zai samu ne idan ka yi wa kotu ɗa’a.”
Wannan jawabin na Wike yana zuwa ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin jihar, inda kafin zaɓen, wata babbar kotun tarayya ta umarci ƴansanda da DSS su tsame hannunsu daga zaɓen, sannan kada INEC ta ba hukumar zaɓen jihar rajistar masu kaɗa ƙuri’a, duk da cewa wata kotun ta sahale wa hukumar zaɓen jihar gudanar da zaɓen.
Bayan zaɓen ne aka wayi gari da tashin-tashina a jihar, inda har aka ƙona wasu daga cikin hedikwatar ƙananan hukumomi guda uku, lamarin da gwamna Fubara ya ce zai ƙaddamar da bincike domin gano waɗanda suke da hannu.
Wike ya ce, “Lokacin da nake gwamna, ina bin doka da oda na kotu. Bin hukuncin kotu dole ne, bai kamata ka ɗauki doka a hannu ba. Da zarar ka yi kunnen uwar shegu da hukuncin kotu, to kana jawo rikici ne.”
Wike ya ƙara da cewa ana zarginsa da yi wa PDP maƙarƙashiya ta hanyar goyon bayan Tinubu, “amma ga gwamnan ya ɗauki nauyin ƴan takara a APP, sannan shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya je rantsar da su.”
A ƙarshe Wike ya ce bai yi da-na-sanin goyon bayan APC a zaɓen 2023 ba.


 

 
 