Ministan Abuja Nyesom Wike ya gana da ‘yanmajalisar jihar Rivers da ke jayayya da ɓangaren Gwamna Fubara, waɗanda kuma aka dakatar.
Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya ce an yi ganawar ne ranar Litinin a birnin Landan.
Wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X ya nuna ministan da ‘yanmajalisar na cin abincin dare tare.
Wike ya tafi Landan ne bayan ganawa da abokan siyasarsa a jihar ta Rivers ranar Lahadi, wadda ke ƙarƙashin dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya saka saboda rikicin siyasa tsakanin Wike da Gwamna Fubara.
A makon da ya gabata ne ‘yanmajalisar suka sanar da yin balaguron zuwa Birtaniya da zimmar inganta ayyukansu na majalisa a can.