Gwamnan jihar Ribas kuma jigo a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike a ranar Asabar ya koma jiharsa, bayan ya kwashe kwanaki a kasar Turkiyya, domin ya samu nutsuwa bayan wani yanayi na siyasa.
Wike, tare da takwaransa na jihar Abia, Okezie Ikpeazu, a ranar Talata, 28 ga watan Yuni, sun tafi kasar Turkiyya hutu, inda daga bisani gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya tare su.
A lokacin da yake kasar Turkiyya, an yi ta rade-radin cewa, ya tashi zuwa kasar Faransa, inda ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda daga baya muksancin sa ya musanta hakan.
Idan dai za a iya tunawa dai a kwanakin baya Wike ya sha kaye a takarar shugaban kasa na jam’iyyar a hannun Alhaji Atiku Abubakar da kuma tikitin mataimakin shugaban kasa a hannun takwaransa na jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
An ce ya ji haushi ne sakamakon matakin da Atiku ya dauka wanda ya yi watsi da shi a matsayin abokin takararsa na zaben Okowa.