Gwamnan jihar Rivers, Nyeson Wike, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 a jam’iyyar PDP.
Wike ya ce, shi ne ya fi kowa iya kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
Wike wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci takwaransa na jihar Benue, Samuel Ortom a gidan gwamnati dake Makurdi, babban birnin jihar Binuwai a ranar Lahadin.
Ya ce, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karon farko a Benue. “Domin kawar da APC daga mulki, ni ne wanda zan iya gaya musu ya isa. Dole ne mu karbi wannan ikon kuma a shirye nake in karba wa PDP. Allah yana tare da mu shi ya sa APC ta ci gaba da gazawa kullum.”
“A shekarar 2015, wadanda suka gudu sun sa mu a zabe. Yau suna kuka amma wasunmu sun tsaya suna cewa PDP ba za ta mutu ba.