fidelitybank

Wike ya bayar da wa’adi kan masu filaye da gidaje a Abuja su biya haraji ko su bar yankin

Date:

Gwamnatin Tarayya ta bayar da wa’adin ne na kwana 14 rak ga masu filaye da gidajen da ke birnin tarayyar da yawansu ya kai 4,794 waɗanda suka yi biris da ƙin biyan haraji ga filayen.

Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Nyesom Ezenwo Wike, ya ce sabon tsarin zai shafi masu filaye da gidaje da kezaune tsakiyar Abuja da aka nemi su biya naira miliyan 5 tare da sauran kuɗaɗen da ake bin su bashi a baya. Sai masu kadarorin a Maitama da Asokoro da Wuse II da Guzape, su kuma za su biya harajin naira miliyan 3, yayin da masu filayen da ke Wuse I da Garki I da Garki II an dora mu su biyan naira miliyan 2.

Ministan ya ce wannan mataki ne da gwamnatin ƙasar ta fito da shi domin tabbatar da masu filaye sun kiyaye dokokin biyan haraji da kuma tafiyar da su yadda ya dace.

Haka ma ministan birnin tarayyar Najeriyar ya ce za su ɗauki matakin ladaftar da waɗanda suka mallaki gidaje da sauran kadarorin da ba su yi musu rajista ba, inda su ma aka ba su wa’adin kwana 14 da su yi wa filayen da sauran kadarorin rajista kafin cikar wa’adin ko su fuskanci ƙwacewa.

Mista Wike ya ce matakan da gwamnatin tarayya na buƙatar a tabbatar da an biya harajin dukan gidaje da filaye akan lokaci kasancewar abu ne mai muhimmanci a ɓangaren bunƙasa birnin na Abuja tare da samar da aikin yi ga jama’a.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp