Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa jihar a na bin ta dimbin basussuka, kuma gwamnatinsa ta gaji dimbin bashi daga tsohuwar gwamnatin Nyesom Wike.
Gwamna Fubara ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin kaddamar da titin Aleto-Ogale-Ebubu-Eteo, (wanda aka fi sani da Old Bori Road a karamar hukumar Eleme ta jihar.
Gwamna da Wike wanda shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, na takun-saka kan yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a jihar.
Duk da shiga tsakani da shugaban kasa Bola Tinubu yayi, Wike da Fubara sun cigaba da caccar baka a tsakanin juna.
Wike a lokuta da dama na ikirarin cewa ya bar jihar ba tare da ya bar mata bashi ba.
Sai dai da yake jawabi a wurin kaddamar da ayyukan da ke Eleme, Gwamna Fubara ya ce, yawancin ayyukan da gwamnatin da ta shude ta kaddamar su ba tare da ta biyan kudaden ba, inda ya kara da cewa ‘yan kwangilar na dawo wa daga baya a biya su hakkin su.
Gwamnan, wanda bai bayar da kiyasin bashin da ake bin jihar ba, ya ce yanzu ya tilasta masa yin magana bayan da masu jifansa da kalamai irin na siyasa ke tunzura shi kuma dole ya amayar.
Wike ya bar wa Ribas tarin ɗimbin bashi – Fubara
Date: