Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ba shi tikitin takarar sanata a lokacin da suka hadu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a safiyar Juma’a.
Gwamnan ya shirya tattaunawar ne a wani yunkuri na magance rikicin jamâiyyar PDP.
A cewar Wike, ya fito takarar shugaban kasa ne saboda yana son zama dan takara, don haka bai sayi fom din takarar Sanata ba.
âBan tsaya takara ba don haka zan iya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa.
“Ni ba kamar wasu da ba su da hankali suka sayi fom din takarar Sanata tare da fom din shugaban kasa, kuma shi ya sa lokacin da Tinubu ya ba ni takarar majalisar dattawa, ban je ba.”