Wata kungiya ta Arewa Youth Advocates for Peace and Unity Initiatives, ta bayyana gwamnan jihar Riba, Nyesom Wike a matsayin wanda ya fi dacewa da dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar.
Kungiyar wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Sani Mohammed, wadda kwafinta ta samu ga Daily Independent a Bauchi a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce idan aka yi la’akari da karbuwar Wike a fadin kasar nan, ya yi fice a tsakanin sauran ‘yan takarar.
“Muna ganin ya dace mu zama abokan aikin ci gaba, Wakilan Samar da zaman lafiya don tabbatar da cewa an wayar da kan matasa ta hanyar dandali na kafafen yada labarai, don kara tabbatar da cewa matasa sun bayar da gudunmawa mai kyau ga ci gaban kasarmu daya tilo ta Najeriya, domin zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.