Matasan Jam’iyyar PDP karkashin inuwar jam’iyyar National Solidarity Vanguard, sun yi zargin cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ke da alhakin haifar da bangaranci a majalisar dokokin jihar Ribas.
Tun a baya dai Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ayyana kujerun ‘yan majalisa kusan 25 da ke biyayya ga Wike.
A yayin da ake fama da rikicin siyasa a jihar, gwamnan ya dage cewa ficewar ‘yan majalisar karkashin jagorancin Amaewhule Martins daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, bas a kan ka’ida.
Kungiyar a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, ta zargi Wike da haddasa rikici a cikin jam’iyyar a matakin kasa da jihohi.
Usman Saidu Calculus, Babban Darakta na kungiyar, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya bayyana Wike a matsayin shi ke cin dunduniyar jam’iyyar tare da yi mata zagon kasa.
Ya kuma ce, ba za su cigaba da daukar Wike a matsayin dan jam’iyyar PDP, bisa yadda ya ke yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Wike na cin dunduniyar PDP – Matasan Jam’iyya
Date: