fidelitybank

Wike da Fayose ba su halarci taron yakin neman zaben gwamnan Osun ba

Date:

Jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP ta gudanar da wani gangami na jam’iyyar, domin tallafa wa dan takararta a zaben gwamnan Osun da ke tafe, Ademola Nurudeen Jackson Adeleke.

Dukkan jiga-jigan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na jihar in ban da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

Sauran wadanda ba su halarci wurin taron sun hada da gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Idan dai za a iya tunawa jam’iyyar ta fada cikin rikici tun bayan bayyanar Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar.

POLITICS NIGERIA ta ruwaito cewa, kwamitin da ya kafa domin tantance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar ya zabi Wike amma abin mamaki shugabannin jam’iyyar da tsohon mataimakin shugaban kasar sun ki amincewa da shi.

Hakan bai yiwa gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom dadi ba, inda yayi gaggawar nuna rashin jin dadinsa da ci gaban da aka samu tare da yin kira ga jam’iyyar da ta tuntubi Wike.

A makon da ya gabata ne wasu gwamnonin APC uku tare da Fayose suka ziyarci Wike a Fatakwal domin lallashinsa zuwa jam’iyya mai mulki da kuma abubuwan da suka faru a yau, ga dukkan alamu rikicin jam’iyyar adawa ya yi nisa.

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp