A ranar Litinin din da ta gabata ne jamâiyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, dan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a matsayin dan kungiyar Kwankwasiyya.
Kwankwaso ya ce Wike a kodayaushe yana tsayawa kan gaskiya, don haka shi dan Kwankwasiyya ne.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen kaddamar da titunan cikin gida na Mgbutanwo a karamar hukumar Emohua ta jihar.
A cewar Kwankwaso: âMai girma gwamna na gode da ka tsaya tsayin daka, ka fadi gaskiya a kowane lokaci, ba tare da laâakari da abin da suke tunani ba.
âMai martaba, ba tare da sanya jar hula ba, kai dan Kwankwasiyya ne a kowace rana, ko wane lokaci. Domin a Kwankwansiyya, ba sai ka sanya jar hula ba. Jamaâa da dama a kasar nan sun samu jajayen hula a cikin zukatansu, kuma na yi imani kana daya daga cikinmu; shi ya sa na yi imanin cewa mu mutanen Kano muna girmama ku sosai.â