Hukumar Lafiya ta duniya ta sanar da amincewa da allurar rigakafin ƙyandar biri na farko.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da aka kai rigakafin MVA-BN zuwa ƙasar DR Congo, ƙasar da cutar ta fi ƙamari.
Akwai kusan mutum 22,000 da suka kamu da cutar a Congo, sannan aƙalla mutum 716 ne suka rasu a yanayi mai kama da cutar.
Zuwa yanzu, an kai rigakafin guda 200,000 zuwa ƙasar ta DR Congo daga Tarayyar Turai, sannan an kai guda 50,000 daga Amurka.
Wata ƙwayar cuta da ake iya yaɗawa daga dabbobi zuwa mutane, sannan mutane na iya yaɗawa zuwa wasu ne ke jawo cutar ta Mpox.
Cutar na jawo zazzaɓi da ƙuraje, sannan a wasu lokuta tana kisa.
WHO ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin cewa, “amincewa da wannan rigakafin zai taimaka a yaƙin da ake yi da annobar cutar ƙyandar biri a Afrika, da kuma kare dawowar cutar a gaba,” kamar yadda Shugaban WHO, Tedros Adganom Ghebreyesus ya bayyana a sanarwar.
“Yanzu abun da muke buƙata shi ne a haɗa da yawa, a samu saya sannan a raba domin sauƙaƙa samuwarsa a wuraren da ake buƙata domin daƙile yaɗuwar cutar da kare rayukan al’umma.”
Amincewar WHO na nufin duba ingancin allura da sauran magunguna, wanda hakan ke ba Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin duniya damar saya da raba su.