Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta bayyana cewa. ta damu matuƙa kan hare-haren da ake kai wa asibitoci da sauran wuraren kiwon lafiya a Ukraine.
Sama da marasa lafiya da kuma jami’an lafiya 70 ne aka kashe tun bayan da aka soma yaƙin Ukraine.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito fili ta haramta kai hare-hare kan wuraren kiwon lafiya sai dai idan wuraren suna taka wata muhimmiyar rawa a yaƙin kamar bayar da mafaka ga mayaƙa masu lafiya.
Rasha ta sha nanata cewa ba dagan-gan take kai hari a wuraren farar hula ba