Masu neman jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa bakwai sun janye tare da mara wa Bola Ahmed Tinubu baya.
Kazalika, ɗan takara Mista Nicholas Felix ya janye don mara wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo baya.
Dukkan ‘yan takarar sun janye ne jim kaɗan kafin fara jefa ƙuri’a a dandalin Eagle Square da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
‘Yan takara 14 ne suka rage a takarar daga cikin 23 da jam’iyyar ta tantance tun farko.
23 da jam’iyyar ta tantance tun farko. In ji BBC.
‘Yan takarar da suka janye wa Tinubu
Masu neman takarar da suka janye wa jagoran APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu sun ƙunshi waɗanda suka fito daga yankinsa na kudu maso yamma da sauran yankuna.
Su ne:
- Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi
- Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio
- Tsohon Gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun
- Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Dimeji Bankole
- Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar
- Uju Ohanenye – mace tilo
- Sanata Ajayi Boroffice
Waɗanda suka rage a takarar
‘Yan takarar da aka jefa wa ƙuri’su ne:
- Yemi Osinbajo (Jihar Ogun)
- Ahmad Lawan (Jihar Yobe)
- Bola Tinubu (Jihar Lagos)
- Tein Jack-Rich (Jihar Rivers)
- Rochas Okorocha (Jihar Imo)
- Tunde Bakare (Jihar Ogun)
- Rotimi Amaechi (Jihar Rivers)
- Emeka Nwajiuba (Jihar Imo)
- David Umahi (Jihar Ebonyi)
- Ogbonnaya Onu (Jihar Ebonyi)
- Ben Ayade (Jihar Cross River)
- Yahaya Bello (Jihar Kogi)
- Ikeobasi Mokelu (Jihar Anambra)
- Ahmed Rufai Sani