Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), a ranar Talata, ta ce, babu daya daga cikin malaman jami’o’inta da a ka biya albashi, tun bayan da kungiyar ta fara aikin masana’antu a watan Fabrairu.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels Television’s Sunrise Daily, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da yunwa a matsayin makami wajen tilasta wa malaman da ke yajin aikin komawa ajujuwa.
Osodeke ya bayyana cewa, an kwashe watanni 6 ba a biyansu albashin, ya ce, gwamnati mai ci ba za ta iya amfani da karfin yunwa wajen ja da ‘yan kungiyar da ke yajin aiki ba.
KARANTA WANNAN: ASUU ta ƙara tsawaita mako huɗu na yaƙin aiki
A cewarsa, gwamnatin tarayya na tunanin hana malaman jami’o’in albashi zai sa malaman jami’o’in durkushewa tare da kawo karshen yajin aikin.
“An gudanar da albashin mu, wannan shi ne wata na shida da ake kin biyan albashi. Sun dauka idan sun rike albashin mu wata biyu ko uku za mu zo bara mu ce ‘pls ku bar mu mu koma bakin aiki.
“Amma mu a matsayinmu na ƙungiyar masu hankali, mun girma fiye da haka. Ba za ku iya amfani da karfin yunwa don ja da membobinmu ba, wanda shine ainihin abin da gwamnati ke yi, “in ji shi.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki domin matsawa bukatunta na samar da ingantaccen tsarin walwala da inganta fannin ilimi da sauran su, lamarin da ya tilastawa daliban Najeriya zama a gida.


