fidelitybank

Watakila sojojin haya ne suka kashe sojojin mu 17 a Delta – Akpabio

Date:

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa, mutanen da suka yi wa sojoji 17 kisan gilla a jihar Delta na iya zama sojojin haya ba wai mutanen yankin Neja Delta ba.

Ya bayyana haka ne a zaman majalisar na ranar Talata, kwana biyar kenan bayan faruwar mummunan harin.

Akpabio ya yi tsokacin ne lokacin da majalisar ta yanke shawarar kafa kwamiti domin gano abin ya janyo kashe sojojin.

Ya ce “Ba na son na yanke hukunci cewa waÉ—an nan mutanen daga yankin Neja Delta suka fito saboda muna mutunta mata da zama masu kayan sarki. Shi ya sa nake cewa abin da za ku nema shi ne a gudanar da cikakken bincike domin gano ko sojojin haya ne daga wasu Æ™asashen da suka zo Najeriya su aikata ta’annatin saboda bana tunanin mutane ne Æ´an Neja Delta.

“Ba ma cikin yaÆ™i. Ko a lokacin yaÆ™i, ba zai yiwu a rasa irin wannan adadi na sojoji ba. Babu wani yanki da zai aikata irin wannan, ba na tunanin Æ´an Neja Delta ne. Don haka, abu na farko shi ne mu lalubo mutanen da suka aikata taÉ“argazar.” in ji Akpabio.

Ya ce kwamitin zai É—auki nauyin tabbatar da cewa an hukunta mutanen da ke da hannu a kisan jami’an.

Tuni dai kalaman na shugaban majalisar suka soma yamutsa hazo a Najeriya inda ƙungiyoyin farar hula da masu amfani da shafukan sada zumunta suke ta bayyana rashin jin daɗinsu ga kalaman na Akpabio.

An kashe sojojin ne a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a yankunan Okuoma da Okoloba da ba sa ga maciji da juna.

dailypostnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp