fidelitybank

Watakila sabon farashin man fetur lita 302 zai fara aiki a watan Fabrairu

Date:

Rahotanni na nuni da cewa watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa Naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa na Fabrairu, kamar yadda majalisar kasa kan tattalin arziki ta bayar da shawara a watan Nuwamba na 2021.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, ta na ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannun ta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.

A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin Naira 162 da 165 a kan kowace lita.

Kwamitin wucin-gadi na majalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton. A cewar BBC

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp