Kocin Liverpool Jurgen Klopp zai bai wa Luis Diaz damar yanke shawara ko zai iya buga wasa a ƙarshen makon nan bayan sace mahaifinsa da aka yi a Colombia.
Klopp ya tabbatar da cewa Diaz, mai shekara 26, ya dawo atisaye ranar Laraba yayin da Reds ke shirin karawa da Luton ranar Lahadi.
An kama Luis Manuel Diaz da matarsa da bindiga a ranar Asabar. An sami mahaifiyar Diaz a Barrancas amma ba a ga mahaifin nasa ba.
“Za mu jira mu ga halin da ya ke ciki sai mu ɗaura daga nan,” in ji Klopp.
“Ba za mu matsa kan lamarin ba – abin ba a hannun mu ya ke ba,” in ji shi.
Gwamnatin Colombia ta ce ‘yan tawayen ELN ne suka yi garkuwa da mahaifin Diaz, lamarin da ya haifar da wani gagarumin bincike na sojoji da ‘yan sanda.
Rahotanni sun bayyana cewa wakilin ƙungiyar ya ce za a sako mahaifin Diaz nan da kwanaki masu zuwa.
Diaz bai taka leda a wasan da Liverpool ta doke Nottingham Forest da ci 3-0 a ranar Lahadin da ta gabata, inda abokin wasansa Diogo Jota ya ɗaga rigar Diaz mai lamba bakwai bayan ya ci wa ƙungiyarsa ƙwallo ta farko.