An tsinci gawar wata mace Soja, Master Warrant Officer a Najeriya, wacce ke aiki a rukunin 651 Base Services Group, ranar Lahadi.
Majiyoyi sun bayyana cewa an samu jamiāar sojin sama a a gidanta da ke Block T5 Flat 8 a Sam Ethnan Air Force Base Ikeja, Legas, bayan ta rataye kanta a cikin dakinta da misalin karfe ,2:00 a ranar 10 ga watan Yuni 2023.
An ce ta rasu ne bayan wasu jamiāan soji uku na Air Provost da suka zo tare da wata tawagar jamiāan domin Éauke gawar zuwa asibitin sojin saman Najeriya na 661.
Majiyar ta bayyana cewa ba a san musabbabin wannan aika-aika ba, inda ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilin mutuwar ta.