Wata sabuwar kungiya mai suna Patriotic Volunteers Association, ta bullo a cikin jam’iyyar APC ta jihar Kano da nufin bayar da gudunmawar samar da sahihin ‘yan takara a 2023.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a madadin kungiyar a wani taron manema labarai da a ka gudanar a cibiyar manema labarai ta jihar, tsohon kwamishinan jihar Kano, Alhaji Ibrahim Dan Azumi Gwarzo, ya bayyana cewa, a yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa, a na ganin akwai bukatar bayar da shawarwari, domin shigar da ka’idojin dimokuradiyya, saboda haka bukatar samar da gaba mai karfi da inganci.
Ya ci gaba da bayyana cewa, manufar kungiyar ita ce samar da ingantaccen tsarin shugabanci nagari da gudanar da mulki bisa ka’idoji na kasa da kasa.
A cewarsa, kungiyar ta na karkashin jam’iyar APC kuma ta na aiki tare da ita.