fidelitybank

Wata Mata ta maka Mijinta a kotun Kaduna saboda yaƙi kai ta Saudiyya

Date:

Wata mata mai shekaru 45, mai suna Karima Nuhu, a ranar Talata ta maka mijinta, Musa Falalu, a gaban wata kotun shari’ar musulunci da ke Rigasa, a jihar Kaduna, bisa zargin kin kai ta ƙasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, matar wadda ke zaune a unguwar Rigasa, ta shaida wa kotun cewa ta yi aure da Falalu tsawon shekara huɗu, amma abinci na tsawon wata biyu kaɗai ya ba ta tun bayan yin auren.

“Ya faɗa min cewa ya rasa aikinsa na direba amma ya samu wani a Saudiyya, inda ya bukace ni da in yi hakuri da kuma yin alkawarin tafiya da ni,” in ji matar.

“A yanzu, ni ke ciyar da kaina. Har ma na aro masa kuɗi domin ya samu biyan kudin tafiyar, amma bayan samun abin da yake so sai ya sake ni,” inji ta.

Ta shaida wa kotun cewa Allah zai mata sakayya tsakaninta da mijin a gobe kiyama.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin, inda ya shaida wa kotu cewa ya saki matar tasa.

Alkalin kotun, Malam Anass Khalifa, wanda ya tabbatar da rabuwar aure tsakanin ma’auratan, ya ce kotun za ta saurari korafe-korafen matar ne idan da a ce ta gansu.

latest news in nigeria today 
2021 ripples

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp