Wata mata ta kashe mijin abokiyar madigonta ta hanyar daɓa masa wuƙa a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Jaridar Punch ta ce, ba a bayyana sunan matar da ta yi kashe Ikechukwu Onuma da aka fi sani da ‘Ayaaya Onye-Obodo’ ba, amma tana aiki a Kwalejin horo na lafiya a Onitsha.
Ta gudanar da wannan aika-aika ne a gidan mutumin a kan titin Ogboli da misalin karfe 9:20pm na daren Talata a birnin Onitsha da ke jihar Anambra.
Marigayi Mista Onuma ya isa gida ba tare da matarsa ta sani ba, inda ya tarar da ita da wata mata akan gado suna sumbatar juna.
Majoyoyi a unguwar sun ce matar mutumumin ƴar maɗigo ce kuma mijin bai sani ba, kuma tana da abokiyar tarayyarta a ɓoye.
An ruwaito cewa abokiyar maɗigon matar tasa ce ta yi sauri ta kai wa mutumin hari da wuka, ta daɓa masa, bayan da wata gardama ta kaure tsakaninsu.


