Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce nan da watanni 24 za a kammala dukkan sassan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Sanata David Umahi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya kai ziyarar duba hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ministan wanda ya samu rakiyar Ministan Kudi da daidaita tattalin arziki Wale Edun ya bayyana cewa gwamnati ta yi sabon wa’adin ne bayan cimma yarjejeniya da dan kwangilar aikin hanyar Julius Berger.
Ku tuna cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da kwangilar ne a shekarar 2018 a kan kammala watanni 36 amma ta kasa cika alkawari.
Umahi, ya dora alhakin jinkirin da aka samu a kan rashin kudi, yana mai tabbatar da aniyar gwamnati na kawo karshen hanyar a kan lokaci.
Ya ce, “Julius Berger ya amince da kammala tafiyar kilomita 15 a kullum saboda an amince da sabuwar ranar.”