fidelitybank

Wasu ƴan Siyasa ne suka yi amfani da zanga-zangar matsin rayuwa wajen kawo ruɗani – Shettima

Date:

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa shugaban kasa na da aniyar ganin ya tallafa wa al’ummar arewacin kasar nan, sai dai akwai mutanen da ke kawo cikas.

Shettima ya fadi hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis.

Mataimakin shugaban ya ce, shugaba Bola Ahmed Tinubu na sane da halin da al’umma ke ciki, kuma yana tausaya masu, “Insha Allah gwamnati na kawo tsare-tsaren ganin cewa, al’ummarmu an ɗauki matakin ƙarfafasu.”

Mataimakin shugaban ya ce, sun ɗauki matakai da suka haɗa da cire ton 42,000 na hatsi domin tallafa wa al’ummar ƙasar da kuma ƙarin mafi ƙarancin albashi daga 30,000 zuwa 70,000.

“Bugu da ƙari, akwai gidauniyar taimaka wa ɓangaren noma, inda aka ware biliyon 100 domin a tallafa wa manoma, miliyan biyar, yanzu haka an fara tallafawa, kamar a Jigawa mun noma alkama kusan hekta dubu 65,000, kuma za a yi noman rani daga watan Nuwamba,” In ji Shettima.

Kashim Shettima ya ce, gwamnatinsu na ƙoƙarin ganin ta samar da zaman lafiya a sassan ƙasar, musamman a Arewa maso Yamma,inda ya ce ansamu sauƙin matsalar tsaro a wasu jihohin arewacin ƙasar, ” An ɗan samu sauƙi a Borno da Yobe.”

Mataimakin shugaban kasar, Sanata Kashim Shettima ya yi zargin cewa waɗansu ƴan siyasa ne suka yi amfani da zanga-zangar matsin rayuwa da ake ci gaba da yi a ƙasar domin haifar da ruɗani.

“Akwai damuwa a ƙasar, amman gaskiya abun zanga-zangar akwai waɗanda suka shigo,don akwai manufarsu a ɓoye, akwai ƴan siyasa da suke da ɓoyayyar manufa, wanɗanda suke so su kawo ruɗani a ƙasar, suna so su jefa ƙasar a cikin rikicin da ba zamu fita a ciki ba.”

Shettima ya ce, suna nan kan bakansu na taimaka wa al’ummarsu domin sun san suna cikin tsananin rayuwa, sai dai ya ce akwai kuma haƙƙin al’umma dake kan hukumomi na kiyaye dukiyoyin al’umma da rayukansu.

Kashim ya yi watsi da zargin da wasu ƴan ƙasar ke yi wa gwamnatinsu na nuna ɓangarenci musamman wajen rabon muƙamai,inda ya ce hakan siyasa ce kawai ” Ministoci 46 ne amman 24 daga arewa ne, manyan shugabannin ma’aikatun gwamnati waɗanda suke da amfani ga arewa, kamar fannin tsaro, da fannin ilimi da noma dukkansu daga ɓangaren arewacin ƙasar suke.”

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce shugaban ƙasar na fifita arewa idan aka yi la’akari da sabuwar hukumar kula da dabbobi da shugaban ƙasar ya samar saboda ƴan arewa su amfana ne.

Shettima ya ce a wajen kasafin kuɗin ƙasar Tinubu ya ba da kaso mai tsoka ga ɓangaren tsaro da ilimi da lafiya. Ya kuma ce suna kan bakansu na shirin samar da matsugunni ga al’ummar da rikici ya raba da muhallansu a arewacin ƙasar.

Mataimakin shugaban Najeriyar, Shettima ya ce suna da kyakkyawan niyyar samar da aikin yi ga matasan ƙasar, “An kawo tallafin karatu, kuma ba sai kasan wani ba, kowane ɗan Najeriya, yana da haƙƙin samun tallafin biyan kuɗin makaranta, Insha Allah zamu samar wa ƴaƴanmu aiki a Arewa.”

Shettima ya ce sun san halin da matasan suke ciki, kuma nan ba da jimawa ba za su yi taron gwamnoni da attajirai da masu ruwa da tsaki na arewacin ƙasar domin fitar da wani tsari da zai taimaka wa yankin.

“Taron da za mu yi ba na shan shayi bane, da cin kaji, muna son a gani a ƙasa ne, kowane attajiri da yake son ya yi taimako ya faɗi me zai kawo, kuma na yi imanin za su taimaka, za kuma mu gayyaci Rabi’u Musa Kwankwaso.”

Shettima ya ce lokaci ya yi da manyan arewacin Najeriya za su haɗa kai, “Duk ɗan siyasar da yake kishin arewa, ba wai sai ya zama mamba na APC ba, babu banbancin addini babu banbancin siyasa ko ƙabila, iya ruwa fidda kai, mu zo mu haɗa kai, idan mun san me muke yi ba mu da matsalar talauci a arewa saboda Allah ya albarkace mu da komai.”

Arewacin Najeriya dai na fama da mastalar tsaro , lamarin da ya raba wasu al’ummomin yankin da muhallansu, ya kuma hana manoma da dama yin noma a gonakinsu.

Duk da iƙirarin hukumomi na cewa suna ƙoƙarin ganin shawo kan matsalar, sai dai wasu ƴan ƙasar na ganin cewa kamar ba da gaske gwamnati ke yi ba musamman idan aka yi la’akari da rahotannin kashe al’umma da sacewa domin kuɗin fansa da kullum ake samu daga arewacin Najeriyar.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp