fidelitybank

Wasu ‘yan majalisa sun nuna shakku a kan matakin CBN

Date:

Wasu ƴan majalisar dattijawa, sun nuna fargaba game da matakin babban bankin ƙasar na taƙaita kuɗin da al’umma za su iya cirewa daga asusun ajiya.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar Phillip Aduda ya janyo hankalin wakilan majalisar kan cewa matakin na CBN zai yi illa ga al’umma musamman ma masu ƙananan sana’o’i.

A nasa tsokacin, shugaban majalisar sanata Ahmed Lawan ya ja hankalin bankin na CBN da ya yi nazari kan lamarin kafin yanke hukunci kai-tsaye, kasancewar matakin zai shafi mutane da dama.

Ya kuma ce, akwai buƙatar a tattauna da bankin domin samun cikakken bayani kan tsarin, sannan ya buƙaci kwamitin kula da harkar bankuna na majalisar ya tattauna kan batun a lokacin zaman tantance mataimakan shugaban bankin, wanda ake sa ran yi a mako mai zuwa.

A ƙarƙashin sabon tsarin na CBN, ɗaiɗaikun mutane na da damar cire naira 100,000 ne kacal a mako, yayin da kamfanoni za su iya cire naira 500,000 a mako.

vanguard newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp