Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wani yaro matashi ɗan shekara 14, wanda ya kashe kansa a ƙaramar hukumar Ningi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar wa BBC da faruwar al’amarin ya ce, yaron ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa a wani kangon ɗaki.
Mahaifin yaron ne ya sanar da ƴan sanda, game da makomar ɗansa. Kuma ya ce, yaron ya na fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa.
“Bayan sanar da ƴan sanda nan take jami’anmu suka nufibwajwn da al’amarin ya faru, kuma aka ɗauki yaron zuwa babban asibitin Ningi, amma aka tabbatar da ya mutu.” in ji Ahmed.
Rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce, ta ƙaddamar da bincike, domin gano dalilin da ya sa yaron ya kashe kansa.