Kotun laifuka na musamman da ke Ikeja ta sallami wani Tela mai suna Femi Kazeem, mai shekaru 32 wanda aka daure shi a gidan gyaran halin Kirikiri, bisa zargin sa da laifin fashi da makami .
An zargi Kazeem da fashin wayar wani mutum ne yayin da ya yi amfani da wani karfe tare da yi wa wata mata fashin jaka daga hannun ta a ranar 28 ga watan Augustan 2018.
Alkalin Justice Oluwatoyin Taiwo ta saki Kazeem ne saboda masu karar sun kasa gabatar da shaidu, bayan lauyan mai kara, O. A. Bajulaiye-Bishi, ya ce, ba a ga daya daga cikin shaidun ba, dayan kuma ba ya da ra’ayin bayar da shaidar.
Femi Kazeem, ya kwashe shekaru 3 a gidan gyaran halin Kirikiri, a cewar Premium Times.