Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba, kuma mazaunin Lekki Face One, a unguwar Eyenkorin a Ilorin babban birnin jihar Kwara, a ranar Lahadi ya kona gidan sa.
Mummunan lamarin, a cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hakeem Adekunle, a Ilorin ranar Lahadi, ya faru ne da misalin karfe 10:28 na safe.
Ya ce, wani Mista Kola da ke zaune a unguwar shi ne ya yi gaggawar kiran hukumar kashe gobara don tashin gobarar.
Jami’an kashe gobara na jihar Kwara sun kashe gobarar a kan lokaci tare da hana ta tashi zuwa wasu gine-gine.
DAILY POST ta rawaito cewa, mutumin ya ce: “da gangan ya fesa man fetur a dakunan nasa guda uku, sannan ya banka wuta saboda takaicin matarsa.”
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kara sanya ido a gidajensu ko ofisoshinsu.