fidelitybank

Wani jirgin kasa ya kuma gaucewa a Abuja

Date:

Kasa da mako guda bayan da jirgin kasa da ke zirga-zirga tsakanin Itakpe zuwa Warri, a daidai garin Warri, wani jirgin kasan ya goce a Abuja.

Rahotanni na cewa jirgin ya goce ne a unguwar Kubwa da tsakar ranar Juma’a lamarin da ya rutsa da daruruwan fasinjojin da ke cikin jirgin.

Najib Jibril, wani fasinja ne da ke cikin wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zai tafi Kaduna. Ya shaida wa BBC cewa gocewar ta hana nasu jirgin wucewa.

“Ni da wasu fasinjoji muna cikin jirgin da zai kai mu Kaduna, sai muka isa tashar Kubwa inda kamar yadda aka saba, jirginmu ya tsaya yana jiran wanda ya taso daga Kaduna yazo ya wuce.”

Bayan wani lokaci suna jira, sai jirgin da ya taso daga Kaduna ya isa wurin da suke jira.

Fasinjan ya ce, “Yayin da muke jira, sai kwatsam kan da ke jan taragun jirgin ya goce, kuma tun da taragun ba su gama wucewa baki dayansu ba, sai ya kasance sun hana namu jirgin wucewa.”

Sai dai babu bayani kan dalilin da ya janyo gocewar jirgin kasan, amma an ga fasinjoji na yawo a wurin da jirgin ya lalace.

Wata majiya a ma’aikatar Sufuri ta Najeriya ta tabbatar wa BBC aukuwar hadarin.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp